Buhari ya ziyarci Deby a Chadi

Hakkin mallakar hoto Buhari Office
Image caption Shugaba Buhari da shugaba Idris Deby

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ziyarci kasar Chadi domin tattauna yadda za a magance matsalar tsaro da ke addabar kasashen biyu.

Ya tattauna da shugaba Idris Derby a birnin Ndjamena, kan yadda kasashen masu makwabtaka za su ci gaba da yaki da kungiyar Boko Haram.

Ziyarar ita ce ta biyu da zai kai wata kasa, inda a ranar Laraba ya gana da takwaransa na Nijar, Mahammadou Issoufou duk a kan lamarin yaki da Boko Haram.

Buhari a Nijar ya ce yana da kwarin gwiwa dakarun Nigeria za su murkushe 'yan Boko Haram.

Hare-haren 'yan kungiyar ta Boko Haram dai suna kara kamari a kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru, musamman a jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.