Gobara ta hallaka mutane 96 a Ghana

Image caption Gobarar ta lalata gidaje da dama

Mutane kusan 96 ne suka rasa rayukansu a sakamakon wata gobara da ta tashi a wani gidan mai a Accra babban birnin kasar Ghana.

Gobarar ta tashi ne a yayin da ake tafka wani ruwa kamar da bakin kwarya wanda ya tilastawa mutane fakewa a gidan man.

Ruwan da aka tafka a haddasa ambaliya a wurare da dama abun da kuma ya dakatar da komai a Accra babban birnin kasar ta Ghana.

A lokacin da ya kai ziyara wurin da hatsarin ya afku, shugaban Ghana, John Mahama ya ce, babu wasu kalamai da za su iya bayyana yadda ya ke ji saboda abun da ya ganewa idanunsa.

Tuni dai ya yaba wa ma'aikatan ceto wadanda suka hada da sojoji da 'yan sanda da kuma 'yan kwana-kwana a kan bajintar da suka nuna.

Image caption Gidan man da ya kama da wuta
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Hakkin mallakar hoto BBC World Service