Google ya yi katobara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Google ya ce ya yi kuskure ne

Katafaren kamfanin Intanet na Google, ya nemi gafara daga Firayi Ministan India, Narendra Modi, bayan da hotonsa ya bayyana a sakamakon wani bincike na manya-manyan masu tafka laifi goma na duniya.

Kamfanin ya ce an samu wannan kuskure ne saboda yanayin da ake bayyana hotuna a Intanet yana iya bayar da samako bai ban al'ajabi ga wasu binciken da ake gudanarwa.

Hoton na Narendra ya fito baro-baro tare da hotunan Osama Bin Laden da kuma mutumin nan Dawood Ibrahim wanda ake zargi da kai harin bam na Mumbai a shekara ta 1993.

Neman gafara ta kamfanin google ta zo ne bayan da yan siyasa masu yawa a India da masu sharhi suka bayyana damuwarsu a shafukan sada zumunta.

To sai dai duk da neman gafarar har yanzu hoton na Mr Modi ya na fitowa a jerin hotunan mutane goma da suka fi tafka manya manyan laifuka a duniya.