Saudiyya za ta ba da tukwici

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A watan da ya gabata ne aka kai harin kunar bakin wake masallan shi'a a Saudiyya

Saudi Arebiya ta yi alkawarin bayar da tukwici na kimanin dala miliyan biyu ga duk wanda ya taimaka wajen kamo 'yan ta'adda ko kuma ya taimaka wajen kare hare-hare.

Hukumomin Saudiyya sun sanar da alkawarin kudin ne a yayin da suka lissafa sunayen mutane 16 da ake zargi da hare-haren kunar bakin wake da aka kai wasu masallatan mabiya shi'a biyu a watan da ya gabata.

An kai hare-haren ne dai a yayin da ake gabatar da sallar Juma'a a masallatan.

Kungiyar masu da'awar jihadi ta IS reshen Saudiyya ta dauki alhakin kai hare-haren, wadanda ke barazanar kawo rashin zaman lafiya ga al'ummar 'yan tsirarun mabiya shi'a na kasar.

Kungiyar IS na kokarin kafa daula a kasashen Syria da kuma Iraki.