Korea na daukar matakai kan cutar MERS

Yaki da cutar MERS a Korea ta Kudu Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yaki da cutar MERS a Korea ta Kudu

Kasar Korea ta Kudu, ta rufe makarantu sama da 500 a wani bangare na kokarin hana yaduwar annobar nan da ta barke ta cutar da ke shafar numfashi wadda ta samo asali daga yankin Gabas ta Tsakiya watau MERS.

Mutane biyu ne dai suka mutu akwai kuma karin wasu biyar da suka kamu da cutar, abinda ya kai adadin zuwa 35 na mutanen da ke dauke da cutar a kasar.

Korear ta Kudu dai ta zamo kasa ta farko da aka samu mutane da dama da suka kamu da cutar bayan Saudi Arebiya, kasar da tun farko aka gano cutar.

Bayan ta gana da hukumomin lafiya na kasar, Shugabar Korea ta kudu Park Gun-Hye, ta yi kiran da a kara tashi tsaye wajen kare yaduwar cutar da rage fargaba a zukatan jama'a.

Karin bayani