Mutane 38 sun mutu a kasuwar Jimeta

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption Ana zargin kungiyar Boko Haram da kai hare-haren

Rahotanni daga jihar Adamawa sun ce a kalla mutane 38 ne suka mutu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a kasuwar Jimeta da ke Yola babban birnin jihar.

Harin ya auku ne a kofar babbar kasuwar Jimeta bayan an fito sallar Magriba a ranar Alhamis, a dai-dai lokacin da 'yan kasuwar suka rufe rumfunansu.

Kusan mutane 40 ne suka ji raunuka sakamakon harin.

A jihar Borno ma, rahotanni sun ce wani dan kunar bakin waken ya kai hari a wani wurin binciken ababen hawa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu.

Hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA ce ta tabbatar da wannan adadin a wata hira da BBC.

Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin, amma ana zargin Boko Haram saboda ta sha kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Nigeria.