Mutane 175 sun mutu a gobarar Ghana

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ambaliyar ta yi ta'adi sosai a Accra

Adadin wadanda suka mutu sakamakon gobara da ambaliyar ruwa a birnin Accra na kasar Ghana, ya kai mutane kusan 175.

Tuni dai gwamnatin Ghana ta ayyana makokin kwanaki uku sakamakon wannan bala'i da ya auku a ranar Laraba.

Gobarar ta tashi ne bayan mutane da dama sun nemi mafaka a wani gidan mai, a lokacin da ruwan saman da ya sauka kamar da bakin kwarya.

Shugaba John Mahama na Ghana ya sanar da cewa gwamnati za ta kashe kusan dala miliyan 12 a kan ayyukan jin-kai, da kuma gyara abubuwan more rayuwa da suka lalace.

Wakilin BBC a Ghana ya ce ko da yake harkoki sun fara kankama bayan wannan ibtila'i, sai dai har yanzu jikin mutane a sanyaye yake.