Malala: An saki mutane takwas

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Malala na ci gaba da rayuwarta a Ingila

'Yan sanda a Pakistan sun amince cewa takwas daga cikin mutane goma wadanda aka ba da labarin an tsare su a gidan yari saboda yunkurin hallaka Malala Yousafzai mai rajin kare hakkin yara an sake su.

Babban sufetan 'yan sanda na yankin Swat Valley, Azad Khan ya ce a cikin mutanen goma da aka gurfanar gaban shari'a an sallami takwas daga cikin su.

Matakin ya biyo bayan rashin cikakkiyar shaida a wani hukuncin da aka yanke a watan Afrilu.

Malala ta kasance mai rajin kare hakkin bil'adama domin baiwa mata 'yan zuwa makaranta a Pakistan.

Da farko hukumomin Pakistan, sun fada a wancan lokaci cewa dukkan mutanen goma an yi musu daurin rai da rai.