Nijar ta sanya hannu kan dokar bauta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Nijar Muhammadu Isufu

Kungiyar kwadago ta duniya ILO na gudanar da wani taro a birnin Geneva, domin tattanawa da kuma rattaba hannu kan dokar kawar da bauta a kasashen duniya.

Wakilai da kungiyoyin daga kasashe daban-daban ne ke halartar taron.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen da ke fama da matsalar bautar da mutane, inda ko a kwanakin baya ma ta rattaba hannu kan dokar kawar da bauta a kasar.

Alhaji Mustapha Khadi shine shugaban kungiyar RDM mai yaki da bautar a Jamhuriyar Nijar ya kuma ce "Mun yi farin ciki da wannan taro saboda zai sa Nijar ta fita daga sahun kasashen da ke fama da wannan matsala a duniya."

Miliyoyin mutane ne ke cikin kangin bauta a duniya.