Saudiyya ta tare makamin da aka harba mata

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saudiyya na fuskantar barazana daga 'yan tawayen Yemen

Saudi Arabiya tace ta tare wani makami mai linzami da 'yan Tawayen Houthi suka harba cikin kasar daga Yemen

Hukumomi sunce an harba makamin ne saitin birnin Khamees Mushait da sanyin safiyar amma an harbo makamin

Harin dai na zuwa ne bayan da kamfanin dillacin labarun Saudiyyan ya ruwaito cewa an dauki sa'oi da dama ana gwabza fada a jiya jumu'a akan wasu yankunan kasar dake kan iyaka

Kamfanin dillacin labarun yace an kashe 'yan saudiyya hudu a fafatawar da kuma Yemenawa da dama, yayinda sojojin saudiyyan suka murkuse farmakin, wanda 'yan Tawayen Houthi da kuma sojojin dake biyayya ga Tsohon Shugaban Yemen Ali Abdallah Saleh suka kai

Mazauna babban birnin kasar Yemen na Sana'a sunce kawancen sojojin dake karkashin jagorancin Saudiyyan yayi ta luguden wuta a birnin daga bisani