Bincike kan kisan Bafaranshe a Najeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jami'in dan sanda a Najeriya

A Najeriya, rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta cafke mutane 30 a binciken da take gudanarwa game da kisan da aka yi wa wani tsohon sojan Faransa a garin Abomoge.

Lamarin ya auku ne yayin da tsohon sojan mai suna Magnan Dennis mai shekaru 62 a duniya da matarsa, mai shekaru 53, suka yada zango cikin dare a wani daji, a kan hanyarsu ta zuwa Kamaru daga birnin Legas a motarsu.

Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta ce bayan mutumin da matarsa sun yada zango ne, wasu mutane uku dauke da makamai suka afka musu, inda suka harbi tsohon sojan a kafa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Mista Maigari Dikko ya ce an wuce da gawar tsohon sojan Legas domin mayar da ita kasar shi.