Shugaba Buhari zai halarci taron G7

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai je kasar Jamus domin halartar taron kungiyar kasashe 7 masu karfin tattalin arziki da za a bude a Bavaria.

Mai magana da yawun shugaban Mallam Garba Shehu a cikin wata sanarwa ya ce duk da cewa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ce ta gayyaci Muhammadu Buhari, shugaban na Najeriya ba zai shiga cikin tattaunawar tsundun ba saboda Najeriya, bata cikin kungiyar ta kasashe 7 masu karfin tattalin arziki.

Mallam Garba Shehu ya ce Shugaba Buhari, yana daga cikin sauran shugabannin kasashe da aka gayyata a matsayin baki.

A gobe Litinin, mahalarta taron zasu tattauna barazanar da ake samu daga kungiyoyin irin su IS da Boko Haram da shugabannin Najeriya da da Tunisia da Iraki.