G7:Obama ya bukaci matsa kaimi akan Rasha

Obama da Merkel suna gaisawa a taron G7 a Jamus Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Obama da Merkel suna gaisawa a taron G7 a Jamus

Shugaba Barack Obama da shugabar gwmnatin Jamus Angela Merkel sun tattauna a taron kolin shugabannin kasashe na kungiyar G7 masu cigaban tattalin arziki na duniya dake gudana a Bavaria a kudancin Jamus.

Da yake awabi gabanin fara taron shugaban Amurka Barack Obama ya bukaci takwarorinsa shugabannin duniya su tashi tsaye akan abin da ya kira nuna fin karfi da Rasha ke yi a Ukraine.

A nasa bangaren firaministan Burtaniya David Cameron yace ya yi imani wakilan kungiyar tarayyar turai za su amince da tsawaita takunkumi akan Rasha.

A wannan watan ne dai wa'adin takunkumin yake cika.

Shugaban majalisar gudanarwar tarayyar tun Donald Tusk ya yi tsokaci da cewa ana iya karfafa takunkumin