Soji sun gwabza da 'yan bindiga a Kaduna

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya an yi aringama tsakanin jami'an tsaro da wasu da ake zaton 'yan Boko Haram ne a wata unguwa da ke wajen garin Kaduna, wadda ake kira Kekebi.

Mazauna unguwar sun ce tun kimanin karfe daya na daren jiya ne har ya zuwa safiyar yau aka yi ta harbe-harbe tsakanin 'yan bindigar da jami'an tsaro, wadanda suka hada da sojoji da kuma 'yan sandan ciki na SSS.

Mutum daya daga bangaren jami'an tsaron aka ce ya rasu, daya kuma ya sami raunuka.

Wadanda ake zargin kuwa sun arce dauke da manyan bindigogi amma ance an kama matansu.

Wakilin Sashen Hausa na BBC a Kaduna Nurah Mohammed Ringim ya ce mazauna unguwar sun firgita sosai.

Jami'an tsaro sun ce samamen da suka kai a unguwar na daga cikin tsarinsu na yakar masu tada kayar baya.

Karin bayani