'Yan cirani dubu 500 na shirin ketara teku

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan ci rani da aka ceto daga teku

Wani babban jami'in rundunar sojin ruwa ta Burtaniya ya ce alamu na nuna wasu da suke da niyyar tafiya ci rani kimanin dubu 500 suna tattaruwa a Libya domin kasadar ketara tekum Bahar Rum zuwa Turai dake da mugun hadari.

Michael Fallon ya yi gargadin cewa kasashen Turai zasu ci gaba da fama da kwararowar 'yan ci rani har sai sun hada kai sun magance matsalar masu fasakwaurin mutane da ke cin riba da rikicin siysar Libya.

Mista Fallon wanda shi ne sakataren tsaron Burtaniya yana daga cikin jami'an da suka yi balaguro ta tekun na Bahar Rum kuma ya ce sun hango 'yan ci rani fiye da dubu uku a kan tekun.

Ya ce kasashen Turai zasu iya toshe hanyoyin da masu fasakaurin mutanen ke samun kudade, domin hanasu ci gaba da mugunyar sana'ar.

A jiya Asabar ne jiragen ruwa na yaki da kuma masu gadi a saman teku suka ceto a kalla 'yan ci rani dubu 2.

Kakakin jami'an Italiya masu gadi a teku Commodore Filippo Marini ya ce wadanda aka ceton, suna daga cikin fiye da 'yan ci rani 3000 da aka hango, wadanda kuma hukumomi suka ga yakamata a kubutar dasu.