'Yan Eritrea na rayuwa cikin fargaba

Image caption Ana zargin Afewerki da kama karya

Majalisar dinkin duniya ta ce, gwamnatin Eriteria ta na gudanar da wani tsari na tauye hakkin bil'adama.

Bayan wani dogon bincike da aka gudanar, hukumar majalisar dinkin duniyar ta ce, wani tsarin iko da rayuwar jama'a ya sanya al'ummar Eriteria yin rayuwa cikin halin fargaba.

Binciken ya ce, irin wannan hali ya tilastawa dubban 'yan kasar gudun hijira a wasu kasashen.

Eriteria dai ita ce ta biyu, a wayan jama'ar da ke kokarin tsallaka tekun bahar rum domin gudun hijira.

Rahoton ya kuma ce, ana yi wa mutane gallazawa kamar, kamu haka kawai, da dauri, da azabtarwa.

Shugaba Isaias Afewerki ya shugabanci kasar na tsawon shekaru 22, kuma ba a taba gudanar da zabe a kasar ba, tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai daga kasar Ethiopia a shekarar 1993.