Za a bude cibiyoyin kula da mashaya a Iran

Hakkin mallakar hoto MEHR
Image caption An haramta shigar barasa a kasar Iran tun wani bore da aka yi ta kishin musulunci a shekarar 1979.

Jami'an Iran sun ba da sanarwa bude cibiyoyin kula da wadanda shan barasa ya zamowa jaraba, guda 150 a fadin kasar.

Sashen kula da miyagun kwayoyi ta ma'aikatar kula da lafiyar kasar ta ce sabobbin wuraren da za a bude za su baiwa mutane damar samun taimako domin barin halin shaye-shaye.

An haramta shigar da barasa a kasar Iran tun wani bore da aka yi ta kishin musulunci a shekarar 1979.

Duk da haka ana sarrafa barasa a boye, da kuma safararsa daga kasashen da suke makwabtaka da Iran.

Masu aiko da labarai sun ce shirin da ake yi dangane da cibiyoyin samun kulan, ya nuna cewa jami'an kasar sun tabbatar matsalar shan barasa a kasar ta baci.