An kashe 'yan bindiga 19 a Pakistan

Hakkin mallakar hoto s
Image caption 'Yan bindiga a Afghanistan

Jami'an soja a kasar Pakistan sun ce an kashe a kalla 'yan bindiga goma sha tara a wani fadan bindiga a arewacin Waziristan wanda ke kusa da iyakar Afghanistan.

Jami'an sun ce an kuma kashe sojoji bakwai a lokacin da daya daga cikin 'yan bindigar yayi kunar bakin wake.

Tun shekarar da ta gabata, Pakistan ta ke yaki da masu tada kayar baya a wani yanki mai tsaunika da ke kusa da iyakar Afghanistan.

Pakistan na fama da matsalar 'yan Taliban da kuma mayakan Al-ka'ida abin da ya janyo hasarar rayuka da dama.

A kwanakin baya, sai dai aka yi kashe-kashe tsakanin 'yan Taliban da kuma mayakan kungiyar IS.