G7 za ta taimakawa Nigeria — Buhari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen G7 sun ce zasu duba bukatun Nigeria

A ranar Litinin ne ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai bi sahun shugabannin wasu kasashen duniya wadanda za su yi ganawa ta musamman da shugabannin kasashen duniya masu arzikin masana'antu, wato G7, a Jamus.

Shugabannin kasashen na G7 ne dai suka gayyaci shugaban na Najeriya, wanda suka nemi ya tafi da bukatun kasarsa, domin su duba yiwuwar tamaikawa kasar.

A cewar Shugaba Muhammadu Buhari, shugabannin manyan kasashen na duniya guda bakwai, sun nuna cewa a shirye suke su taimakawa Najeriyar.

Malam Garba Shehu ya shaidawa BBC cewa batutuwa da suka shafi tsaro da cin hanci da rashawa da kuma zuba jari su ne shugaban kasar zai gabatarwa da shugabannin.