Cibiyar sojin Nigeria ta koma Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rundunar sojin za ta fara aii daga Maiduguri.

Rundunar sojin Nigeria ta fara shirye-shiryen mayar da cibiyar da ke jagorantar kai hare-hare zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Shugaban kasar, Muhammadu Buhari ne dai ya ce za a mayar da cibiyar sojin Maiduguri, har sai an karya-lagon 'yan kungiyar Boko Haram, wadanda ke kai hare-hare musamman a arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojin Kanar Sani Usman Kuka Sheka ya shaida wa BBC cewa tuni rundunar ta aike da wasu sojoji da kayyakin aiki, kuma a ranar Litinin za a fara gudanar da cikakken aiki daga jihar.

'Yan kungiyar ta Boko Haram dai sun kashe dubban mutane, yayin da fiye da mutane miliyan uku suka gudu daga gidajensu saboda tsoron hare-haren kungiyar.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 15,000 cikin shekaru shida a Nigeria.