'Yan gudun hijira na son yin azumi a gida

Image caption 'Yan gudun hijira a Najeriya

'Yan gudun hijirar Najeriya da suka rage a garin Fotokol na Jamhuriyar Kamaru sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta mayar da su gidajensu domin su fara yin azumin watan Ramadan da ke tafe.

Watanni goma ke nan ragowar 'yan gudun hijirar ke ci gaba da rayuwa a Fotokol da ke kan iyaka a tsakanin Kamaru da Najeriya.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Najeriya ta ce kwashe akasarinsu, ta kuma mayar da su sansanin Minawao a cikin Kamaru domin a ba su kulawa.

'Yan gudun hijira da suka zabi zama a Fotokol suna yin wasu sana'o'i domin su ciyar da kansu da kuma iyalansu.