Matasan Soweto sun kwashi ganima

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan unguwa suna wawusar kaya daga kantina

An wawushe shaguna da dama a Soweto, daya daga cikin manyan garuruwan da ke Afrika ta Kudu a yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a a kan wani rikici da ake yi a kan wutar lantarki.

Bayan a wawushe kayan wani shagon barasa da kuma na cin abincin kwalama watau KFC, 'yan unguwan kuma sun yi kokarin fasa na'urar cire kudi ta ATM amma kuma 'yan sanda sun fatattake su amma kuma duk sun tsere ba tare da komai ba.

Kamfanin samar da hasken wutar lantarki ta Eskom ta na barazanar yanke musu wuta idan har mazauna yankin ba su canza zuwa mitar sai ka biya kafin ka sha ba.

Mazauna Soweto sun ce sabon mitar na tsawalla kudin wutar lantarkin da suke sha.

Kamfanin Eskom ya ce yana bin mazauna unguwa kusan dala miliyan 636 da suka sha wuta suka ki biya.