Dan sandan Amurka ya shiga uku

Image caption Bakaken fata na zargin 'yan sanda da nuna bambamci a Amurka

An dakatar da wani dan sanda farar fata daga aiki a birnin Texas na Amurka, bayan an saka wani bidiyo a shafin intanet da ke nuna irin yadda ya yi wa wasu matasa, wadanda akasarinsu bakaken fata ne.

An ga dan sandan ya na nunawa wasu matasa biyu bindigarsa.

Mazauna yankin ne dai suka kira 'yan sanda ne bayan sun yi korafin cewa suna jin wata hayaniya a wani wajen wasan nunkaya.

Babban jami'in 'yan sandan yankin, McKinney ya ce yana gudanar da bincike kan lamarin.

Hakan na zuwa yayinda ake zaman dar dar a wasu al'ummomin bakaken fatar Amurka game da cin zalin da 'yan sanda suke yiwa bakar fata.

Shi ma magajin garin ya ce wannan lamarin ya sa shi cikin damuwa.