An kashe mutane 15 a kauyen Borno

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption Mayakan Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare tun bayan rantsar da sabuw\r gwamnati

Akalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu yayin da mayakan Boko Haram suka kai hari kauye Huyum da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Wani wanda ya shaida faruwar lamarin ya gaya wa BBC cewa mayakan sun kona gidaje da dama sannan kuma suka kashe mutane.

"A ranar Litinin da daddare ne suka zo da babura da motoci da yawa kuma sun yi barna sosai, na ga gawarwaki 11 da idona," a cewar mutumin, wanda ya nemi a boye sunansa.

Sai a ranar Talata ne aka samu labarin faruwar lamarin saboda rashin hanyoyin sadarwa a garin.

Kauyen na Huyum na karkashin karamar hukumar Askira Uba ne a jihar ta Borno.