Nigeria: Buhari zai gana da 'yan majalisa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Buhari zai gana da 'yan majalisu na jam'iyyar APC

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, zai gana da 'yan majalisun dattawa da na wakilan kasar na jam'iyya maimulki wato APC ranar Talata a Abuja, babban birnin kasar.

Hakan kuwa ba ya rasa nasaba da dambarwar da ta kaure tsakanin 'yan majalisar game da zaben shugabannin majalisun dattawa da na wakilan kasar da ake sa ran gudanarwa idan anjima.

A baya dai jam'iyyar APC ta fito da Sanata Ahmed Lawal a matsayin dan takararta na shugabancin majalisar dattawa, sannan ta zabi Femi Gbajabiamila a matsayin dan takarar nata daga bangaren majalisar wakilai.

Sai dai wasu 'yan jam'iyyar sun yi watsi da matsayin jam'iyyar, suna masu cewa su ne ke da alhakin zaben mutane da za su shugabance su.