Shin wanene Bukola Saraki ?

Hakkin mallakar hoto bukola
Image caption An zabi Bukola Saraki ne duk da cewa jam'iyyar APC ba shi take so ba.

An haifi Sanata Abubakar Bukola Saraki ne ranar 19 ga watan Disamba na shekarar 1962 a garin Ilorin na jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

Sanata Bukola da ne ga Alhaji Abubakar Olusola Saraki, fitaccen dan siyasar kasar, kuma tsohon shugaban majalisar dattawa.

Ya yi karatunsa a King's College, Lagos daga 1973 zuwa 1978, da kuma kwalejin Cheltenham a London, tsakanin 1979 zuwa 1981.

Haka kuma ya yi digirinsa na farko a fannin likitanci a Kwalejin kiwon lafiya ta asibitin London tsakanin 1982 zuwa 1987.

'Siyasa'

Ya shiga harkokin siyasar Najeriya a shekarar 2000, kuma ya yi takarar gwamna, inda aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Kwara a shekarar 2003, sannan aka sake zaben sa a shekarar 2007.

Haka kuma Sanata Saraki ya zama dan majalisar dattawan Najeriya a shekarar 2011, kuma an sake zaben sa a shekarar 2015.

An zabe shi a matsayin shugaban majalisar dattawa babu hammaya a ranar 9 ga watan Yunin 2015.