An tsamo gawarwaki 30 a kogin Kamaru

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hatsarin jirgin ruwa a Cameroon

Hukumomi a kasar Kamaru sun tsamo gawarwakin mutane sama da 30 daga cikin kogin Lagdo da ke arewacin kasar.

Mutane sun gamu da ajalinsu ne bayan kwale-kwalen da suke ciki ya yi hatsari sakamakon ruwan sama kamar-da-bakin-kwarya da aka yi, wanda ya yi sanadiyar kifewar kwale-kwalen.

Rahotanni sun ce kwale-kwalen ya tashi da akalla mutane 50, kuma kafin su kai masaukinsu ya kife.

A yanzu haka ana ci gaba da neman sauran gawarwakin duk da cewa ana kyautata zaton mutane takwas sun tsira.