An zabi Dogara a majalisar wakilai

Hakkin mallakar hoto DOGARA TWITTER
Image caption Sabon shugaban majalisar wakilai ta kasa, Honorable Yakubu Dogara

An zabi dan majalisar wakilai daga jihar Bauchi, Honorabul Yakubu Dogara a matsayin sabon shugaban majalisar wakilai.

Dogara, wanda ke wakiltar mazabar Bogoro da Tafawa Balewa, ya samu kuri'u mafi rinjaye ne bayan ya fafata da Honorabul Femi Gbajabiamila.

Mista Dogara ya samu kuri'u 182 a yayin da Gbajabiamila ya samu kuri'u 174.

Hakan ya saba da matakin da uwar jam'iyyar APC ta dauka wadda ta umurci 'ya'yanta su zabi Gbajabiamila daga jihar Lagos.

Tun da farko shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gayyaci 'yan majalisar domin su tattauna kan yadda za a shawo kan barakar da ta kunno kai.