Rayuwa karkashin mayakan IS a Mosul

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan IS na kara kame ikon yankuna a Iraki da Syria

Shekara guda bayan da mayakan kungiyar IS suka kwace ikon garin Mosul, wani bincike da BBC ta gudanar ya yi karin haske kan yadda kungiyar ke juya akalar rayuwar mutane a yankin.

An rufe yawancin makarantu yayin da wadanda bude kuma aka tilasta musu koyarwa da jadawalin kungiyar IS.

Dole mace ta rufe jikinta gaba daya idan za ta fita kuma dole ta kasance tana tare da muharraminta.

A dalilin haka farashin hijabai ya karu sosai.

An yanke hanyoyin sadarwa saboda mayakan na son yanke hulda da ko ina tare kuma da sanya dabaibayi kan yadda ake samun labarai.

An tsanantawa mabiya Shi'a da mabiyan sauran addinai da kuma sauran kungiyoyi marasa rinjaye, kuma wasu yankunan birnin da mutane ke zaune yanzu babu kowa a wajen.

Mayakan sun kuma lalata masallatai da dama wadanda suka ce wajen lalata ne ba wajen ibada ba.