Saraki ya zama shugaban majalisar dattawa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sanata Saraki a lokacin da yake shan rantsuwa

An zabi tsohon gwamnan jihar Kwara, Sanata Abubakar Bukola Saraki a matsayin sabon shugaban majalisar dattawan Nigeria, zubi na takwas.

Ya zama sabon shugaban a zaben da ya lashe babu hammaya bayan da Sanata Ahmed Sani daga jihar Zamfara ya gabatar da sunansa.

Saraki, tsohon dan jam'iyyar PDP ne kafin ya koma sabuwar jam'iyyar APC da aka yi hadaka tsakanin jam'iyyun ACN da CPC da kuma wani bangare na APGA.

Haka kuma an zabi, Sanata Ike Ekweremadu a matsayin sabon mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Ekweremadu daga jihar Enugu ya lashe zabe da kuri'u 54 a yayinda Sanata Muhammed Ali Ndume daga jihar Borno ya samu kuri'u 20.

Abin da hakan ke nufi shi ne cewar jam'iyyar adawa ta PDP ta samu kujerar mataimakin shugaban majalisar.