Saraki ya rantsar da Lawan, Akume

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sanata Bukola Saraki ya bijirewa umurnin jam'iyyar APC

Shugaban majalisar dattijan Nigeria, Abubakar Bukola Saraki ya rantsar da wasu sanatoci wadanda suka kaurace wa zaman da aka yi a ranar Talata.

Daga cikin wadanda aka rantsar hadda Sanata Ahmed Lawan, George Akume da Shehu Sani da Remi Tinubu da sauran sanatocin da suka tafi wajen taro tare da shugaba Muhammadu Buhari.

Ita dai jam'iyyar APC mai rinjaye cewa ta yi a zabi Sanata Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa da Honorabul Femi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisar wakilai.

Sabanin hakan dai Sanata Bukola Saraki aka zaba a matsayin shugaban majalisar dattawa, yayinda aka zabi Honorabul Yakubu Dogara a matsayin kakakin majalisar wakilai.

A martaninsa, shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa a shirye yake ya yi aiki da duk wadanda 'yan majalisar suka zaba a matsayin shugabanninsu.