China za ta rage gurbatar muhalli

Shugaban China game da sauyin yanayi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban China game da sauyin yanayi

Wani rahoto na bincike da aka gabatar a Makarantar nazarin darussan harkokin tsimi da tanadi dake London, ya nuna cewar China, za ta yi matukar rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli cikin shekaru goma masu zuwa.

Shekaru biyar kenan kasa da lokacinda aka yi hasashe, kuma wannan cigaba ne kwarai, zai kuma karfafa gwiwa ga kokarin da ake yi na kare muhalli.

Wannan canji na lokacin da aka samu ya biyo bayan namijin kokarin da Chinar ke yi wajen kago na'urori masu amfani da hasken rana,domin a yanzu Chinar ta yi ma dukkan kasashen duniya zarra wajen saka jari a wannan fanni na samar da naurori masu amfani da hasken rana da masu samar da wutar lantarki ta iska.

A yanzu haka, tana cigaba da maye gurbin injunan ta da wadannan sabbin naurori masu amfani da hasken rana.

Mafi yawan canje-canjen da aka samu a dalilin bukatu ne na kokarin kawo karshen matsalar gurbatar muhalli.

Shugabannin China din kuma suna la'akari da illolin da dumamar yanayi zai yi ma yanayi irin kasar su.

Rahoton yace, kokarin da Chinar ke yi na rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli, ya ba ta kyakkywar dama ta kawar da illolin da hayakin ke haifarwa ga yanayi.

Masu binciken da suka wallafa wannan rahoto sun ce taron da za a yi na Majalisar Dinkin duniya nan gaba cikin wannan shekarar game da batun gurbatar muhalli a birnin Paris, zai kara samun nasara idan gwamnatoci a dukkan sassan duniya suka fahimci sauyin yanayin da aka samu a China da kuma tasirinsa ga gurbatar muhalli a duniya.

Suka ce matakan da China ke dauka za su kawo gasa a kasunnin duniya ta samun tsaftataccen makamashi, kuma zai nakasa kasashe masu fitar da coal ko gawayi da sauran nau'oi na makamashi.

Shugaba Xi Jimping ya yi alkawari a wata yarjejeniya ta fahimtar juna da suka kulla da Amurka ta rage hayaki mai gurbata muhalli daga nan zuwa shekara ta 2030.

Karin bayani