An kai harin kunar bakin wake a Masar

Image caption An kai harin kunar bakin wake Masar

An kai harin kunar bakin wake a Masar a daya daga cikin wuraren da masu yawon bude ido suka fi ziyarta a birnin Luxor.

Mutane uku ne dai suka yi yunkurin tsallake shingen shiga wurin mai dimbin tarihi.

Wakiliyar BBC ta ce "An kai harin ne a wajen wurin ibada na zamanin da ake kira Karnak, wanda yana cikin muhimman wuraren ziyara a Masar."

Daya daga cikin 'yan kunar bakin waken dai ya ta da bam din da ke jikinsa, dayan kuma an kashe shi ne yayin da ya budewa 'yan sanda wuta.

Ba a dai san ko su waye suka kai harin ba, amma ana dora alhakin irin wadannan hare-hare a kan masu fafutukar Musulunci.