An gurfanar da baki a Malaysia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tsaunin Kinabalu

An gurfanar da wasu baki hudu a wata kotu a Malaysia bayanda aka zarge su da daukar hotuna tsirara a tsauni mafi girma da ke kasar.

Lamarin ya faru ne kwananki kadan kafin girgizar kasa da ta afkawa tsaunin na Kinabalu wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Wani jami'i a yankin ya danganta girgizar kasar da daukar hoton da bakin suka yi tsirara-wanda hakan alama ce ta nuna rashin girmamawa ga tsaunin da al'ummar yankin ke girmamawa.

Hukumomi suna neman wasu baki 6 wadanda su ma suka bayyana tsiraicinsu a kan tsaunin.

Wadanda aka gurfanar da su a gaban kotun da ke jihar Sabah da ke kan tsibirin Borneo - sun hada da wata mata 'yar Biritaniya, da 'yan kasar Canada guda 2 da kuma wani dan kasar Holland.