Amurka za ta tura karin dakaru a Iraki

Sojin Amurka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojin Amurka a Iraqi

Shugaban Barrak Obama ya amince a aika dakarun Amurka dari hudu da hamsin domin su ba da horo ga sojojin Iraqi, tare da ba da shawarwari a yakin da ake yi da kungiyar IS.

Dakarun na Amurka za su kasance ne a yankin Anbar, inda 'yan IS suka samu nasarori a baya-bayan nan.

Sai dai dakarun Amurkan ba za su fita bakin daga ba. Ernest Josh,n kakakin fadar White House ya ce wannan mataki ne na karfafa dabarun Amurka na tallafawa dakarun Iraqi a yakin da suke yi da 'yan kungiyar IS.

Fadar White House ta kuma ce, shugaba Obama ya bada umarnin gaggauta baiwa dakarun Iraqi tallafin muhimman kayan yaki.