Fasahar sake sassan jiki

Mutumin da aka sanyawa sabuwar kafa.
Image caption Mutumen da aka makala wata kafa

Masana kimiyya na Austria sun kirkiro wata kafar mutum, wadda za ta bai wa mutanen da aka datse wa kafafuwansu na ainihi jin tamkar babu bambanci a jikinsu.

Mutumin da aka sanyawa kafar, Wolfang Rangger, wanda ya rasa kafarsa a shekara ta 2007 ya ce, "yadda nake ji a jiki na, kamar ban rasa kafa ta ta ainihi ba".

Farfesa Hubert Egger na Jami'ar Linz ya ce hakan ya yiwu ne saboda naurorin da aka makala a jikin sauran sashe na kafar ta ainihi, suna taba jijiyoyin da ke kai jini kafar.

Ya kara da cewa, wannan shi ne karon farko da aka makala wa wani wanda aka datse wa kafa na'urorin da zai ji tamkar kafar sa ta ainihi ce.

Likitocin tun farko sun fara harhada jijiyoyin jinin da ke cikin tsokar naman kafar majiyyacin wadanda aka jawo zuwa karshen fatar sa.

An makala na'urori shida a kasan kafar domin auna karfin tafin kafar da yadda take juyawa.

Wadannan ne ake hadawa da wata naurar da ke sarrafa su lokaci daya da na'urorin da aka makala a jikin kafar da aka lika wa majiyyacin.

Wadannan na'urori su kan yi karar dake sanya jijiyoyin jinin da suka taba su su motsa, wannan kuma ya kan kai har ga kwakwalwa.

Farfesa Egger ya ce, "wadannan na'urori su kan gaya ma kwakwalwa cewar akwai kafa, don haka mai ita, yana jin cewar yana da kafa a lokacinda yake tafiya.

Wolfgang Ranger, tsohon malamin makaranta wanda ya rasa kafar sa bayan wani gundarin jini ya tsaya masa sakamakon shanyewar wani bangare na jikinsa, yana cigaba da gwada wannan kafa da aka makala masa tun watanni shidda da suka wuce a dakin gwaje-gwaje da gidan sa.

Karin bayani