Nemi tashar rediyon BBC a layin salula a Nigeria

Image caption Za a iya kama tashar rediyon BBC ta hanyar danna wata lambar waya

Masu amfani da wayar salula a Najeriya yanzu za su iya kama tashar rediyon BBC mai watsa shirye-shirye ga kasashen duniya cikin harshen Turanci da Hausa, ta hanyar danna wata lambar waya ta cikin kasar: 01 4405 222.

Tashar BBC mai watsa shirye-shirye ga kasashen duniya ta hada gwiwa da kamfanin ZenoRadio, wanda ke kan gaba a hidimar taimakawa wajen ganin jama'a suna sauraren tashar rediyo a wayoyin salula, domin samar da wata dama ta sauraren sautin tashar ta BBC, yayin duk da aka bukata da harshen Turanci (zabi na 1) da harshen Hausa (zabi na 2).

Masu amfani da wayoyin na salula za su iya sauraren shirye-shiryen rediyon da ake watsawa daga kowanne layin wayar salula a Najeriya.

Rediyon na BBC zai rika watsa shirye-shiryensa kai tsaye cikin harshen Turanci dare da rana.

Zai kuma rika watsa shirye-shiryensa cikin harshen Hausa kai tsaye da karfe shida da rabi (6.30) na safe, da karfe uku (3) na rana, da kuma karfe takwas da rabi (8:30) na dare agogon Najeriya, kana a ci gaba da jin kowanne shiri har ya zuwa lokacin da za a watsa shiri na gaba.

Domin sauraren shirye-shiryen, sai masu amfani da wayoyin salula su kira wannan lambar waya: 01 4405 222 da duk layin da suke amfani da shi a Najeriya, su kuma zabi harshen da suke ra'ayi daga jerin zabin sauti (audio menu) da aka tanada.

Sai dai za a biya kudin kiran waya ga kamfanin da aka yi amfani da layinsa, domin sauraren shirye-shiryen na BBC.

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Masu amfani da wayoyin salula za su kira wannan lambar waya: 01 4405 222 domin jin shirye-shiryen

Kuma farashin kiran na waya, wanda aka saba amfani da shi a Najeriya, ya danganta ne ga tanade-tanaden da kamfanonin waya suka yi da kuma abin da suke bukata mai amfani da layinsu ya biya.

Editan sashen Afirka na BBC, Solomon Mugera, ya ce: "Ita lambar wayar ta 01 4405 222 za ta samar da wata hanya ma fi sauki ta sauraren shirye-shiryen rediyon BBC, wanda kafin yanzu yana iya samuwa ne kadai a Najeriya, ta hanyar kama tashar a akwatunan rediyo, da intanet, da kuma tauraron dan Adam."

Mista Mugera ya kara da cewa "Muna godiya da wannan ci gaba da aka samu, duk wani mai wayar salula a Najeriya yanzu zai iya sauraren rediyon BBC mai watsa shirye-shirye ga kasashen duniya cikin harshen Turanci da Hausa a koyaushe.''

Akwai layukan salula da ake amfani da su yau da kullum a Najeriya har miliyan 132.

Ta hanyar amfani da fasahar kamfanin ZenoRadio, gidan rediyon BBC ya bi wani ingantaccen mataki na kyautata hanyar da jama'a za su iya sauraren shirye-shiryensa, wato duk wani mai amfani da wayar salula zai sami damar kama tashar rediyon da wayarsa.

''Godiya ga BBC da kamfaninmu, yanzu masu saurare za su iya kasancewa da shirye-shiryen BBC masu kayatar da su daga kowanne layin wayar salula a kasar'', inji Morris Berger, babban jammi'in kamfanin ZenoRadio.

Ya kuma kara da cewa, "Kasancewar wannan shi ne kamun ludayinmu na farko a nahiyar Afirka, muna alfahari cewa za mu yi aiki tare da BBC a wannan shiri''.

Ta hanyar kiran wannan lambar waya: 01 4405 222 masu amfani da wayoyin salula a sassa daban-daban na Najeriya suna iya sauraren Shirin Hantsi na Sashen Hausa na BBC da karfe shida da rabi (6.30) na safe, Shirin Rana da karfe uku (3.00) na rana, da Shirin Yamma da karfe takwas da rabi (8.30) na dare duk agogon Najeriya.

Shirye-shiryen BBC da suka yi fice cikin harshen Turanci kuwa, sun hada da Newsday wanda ake watsawa a kowacce safiya tun daga karfe hudu na asuba zuwa karfe 8.30 na safe, da kuma Focus on Africa wanda ake watsawa da karfe hudu na yamma, da karfe shida na yamma, da kuma karfe takwas na dare.

BBC Hausa dai wani sashe ne na tashar BBC mai watsa shirye-shirye ga kasashen duniya.