Boko Haram: Dakaru za su fara aiki a watan Yuli

Hakkin mallakar hoto Buhari Office
Image caption Muhammadu Buhari ya ce hada gwiwa da shugabannin kasashen tafkin Chadi zai kawo karshen Boko Haram.

Shugabannin kasashen yankin tafkin Chadi da Benin sun ce dakarun rundunar hadin-gwiwarsu za su fara aikin fatattakar Boko Haram a karshen watan Yuli.

A sanarwar bayan taron da suka fitar a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, shugabannin kasashen biyar sun sha alwashin bayar da $30m domin samarwa dakarun makamai da sauran kayan aiki na yaki da kungiyar ta Boko Haram.

Shugabannin sun amince a kafa hedikwatar dakarun hadin-gwiwar a birnin N'Djamena na kasar Chadi.

Najeriya za ta jagoranci rundunar

A jawabinsa gabanin fitar da jawabin bayan taron, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce kasarsa ce ya kamata ta rike shugabancin rundunar hadin-gwiwa da za a kafa domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Muhammadu Buhari ya ki amincewa kasashen su rika karba-karba a shugabancin rundunar, yana mai cewa hakan zai bai wa Boko Haram damar ci gaba da kai hare-hare.

"Akwai shawarar a dinga yin karba-karbar shugabancin rundunar na tsawon watanni shida tsakanin kasashe biyar, amma ina ganin cewar hakan zai shafi aikin yaki da 'yan ta-da-kayar-baya," in ji Buhari.

Shugabannin da suka halarci taron su ne Muhammadu Buhari na Najeriya da Muhammdou Issoufou na Nijr da Idris Deby na Chadi da Boni Yayi na jamhuriyyar Nijar da kuma wakilin shugaban kasar Kamaru.