Babban jami'in China zai sha dauri

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Zhou Yongkang na China

China ta yankewa wani tsohon babban jami'in gwamnatin kasar, Zhou Yongkang, hukuncin daurin rai da rai saboda karbar cin hanci da yin amfani da iko ba bisa ka'ida ba da kuma tona asirin kasar.

Yongkang yana daya daga cikin manyan shugabannin jam'iyyar kwaminisanci ta China.

Har zuwa lokacin da ya yi ritaya shekaru uku da suka wuce, yana rike da wani mukami mai matukar muhimmanci wanda yake kula da tsaro na cikin kasar.

An yi shari'ar sa ne a ranar 22 a boye a birnin Tianjin; yanzu aka fitar da labarin.

Rahotanni daga kafar watsa labaran gwamnatin China, Xinhau, sun ce Yongkang ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.