Ghana za ta kara karfin wutar lantarki

Image caption Rashin wutar da ake fama da ita a Ghana ta na kawo koma baya ga kasuwanci da tattalin arziki.

Hukumomi a Ghana sun ce za a kara mega watt 1000 na wutar lantarki a karshen shekarar 2015, domin dakile matsalar rashin wuta da kasar ke fama da ita.

Ministan ma'aikatar samar da hasken wutar lantarki, Kwabena Donkor, ranar Laraba ya ce za su cika alkawarin zuwa 31 ga watan Disamba, idan ba haka ba zai sauka daga mukaminsa.

Wutar lantarki ta zama babbar matsala ga siyasa da tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika sakamakon yawan dauke wutar da ake yi har na tsawon sa'o'i 24, matsalar da ke yin tarnaki ga harkokin kasuwanci da tattalin arzikin kasar.

"Mun fito da hanyoyi da dama domin magance matsalolin. Mun riga mun kafa gine-gine na samar da wutar lantarki a kasar, kuma za mu hanzarta kammala su", in ji Ministan samar da wutar lantarkin a wani taro da aka yi a Dubai.

Ya ce gwamnati na kara fadada gine-ginen samar da wutar lantarki, kuma za ta fito da sababbin tsare-tsaren rarraba hasken wutar ta hanyar amfani da iskar gas, yana mai cewa "gwamnati za ta kara karfin wutar lantarkin Ghana da a yanzu take fitar da nau'in Mega Watt 2850 na wutar".

Wasu masana masu sharhi a kan hasken wutar lantarki dai sun ce suna shakkar Ghana za ta iya dakile matsalar hasken wutar lantarki a wannan shekarar, saboda matsalolin da hukumar wutar lantarkin kasar watau Electric Company of Ghana (ECG), da wasu kamfanoni masu zaman kansu suke ciki.