An shawarci INEC kan sabunta katin zabe

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masana sun ce na'urar tantance masu kada kuri'a ta taimaka wajen samun sahihin zabe a Najeriya a 2015

Masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai sun shawarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, da ta dinga sabunta katin zabe na 'yan kasa na din-din-din aka-akai da kuma ci gaba da bayar wa.

Masu ruwa da tsakin sun ce hakan ya zama wajibi saboda a kaucewa rububin karba daf da lokacin zabe.

Sun bayyana hakan ne a yayin wani taro na kwana biyu da hukumar ta shirya domin yin duba kan rawar da kafofin watsa labarai suka taka a zaben shekarar 2015, a birnin Lagos.

Masu ruwa da tsakin -- wadanda suka ce sun lura da yadda na'urar tantance masu kada kuri'a ta taimaka wajen yin sahihin zaben, -- sun shawarci INEC cewa ta samar da hanyar tattara sakamako ta hanyar amfani da komfuta da kuma yin gyara a sauran shirye-shiryensu gabannin zabuka na gaba.

Kazalika, an shawarci hukumar cewa ya kamata ta dinga wayar da kan mutane a kan yadda za su gudanar da zabe musamman mutanen karkara, a kan lokaci.

Haka kuma a jawabin bayan taro an bukaci kungiyoyin farar hula su hada karfi domin magance yada kalaman batanci a kan intanet da kuma sauran hanyoyin sadarwa na zamani.