Dan tsohon shugaban Iran zai sha dauri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akbar Hashemi Rafsanjani, tsohon shugaban Iran da Ministan cikin gida na Iran.

Dan tsohon shugaban kasar Iran, Akbar Hashemi Rafsanjani zai sha daurin shekara 10 a gidan yari.

Wata kotu ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Mehdi Hashemi Rafsanjani bisa laifuffukan keta dokar tsaro da na yi wa tattalin arziki zagon kasa.

An sa wa iyalan tsohon shugaban kasar ido ne saboda yana goyon bayan masu neman kawo sauyi da suka sha kaye a zaben shekarar 2009.

Masana sun ce za a yi wa hukuncin da aka yanke wa, Mehdi Hashemi Rafsanjani kallon wasu na yi wa mahaifinsa bi ta da kulli domin a bata masa suna.