An zargi Manuel Vall da kashe kudin gwamnati

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Manuel Vall ya nace cewa tafiyar tasa ta shafi aiki ne.

Firai ministan Faransa, Manuel Vall, ya ce ya yi dana-sanin yin amfani da jirgin gwamnati domin kai 'ya'yansa kallon wasan karshe na zakarun Turai a birnin Berlin na Jamus, a karshen makon da ya gabata.

Mista Valls ya nace cewa tafiyar tasa ta shafi aiki ne, tunda shugaban hukumar kwallon kafar Turai UEFA Michel Platini ne ya gayyace shi, amma hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a Faransa.

Ya bukaci zai biya euro miliyan biyu da rabi ga masu karbar haraji na Faransa, domin biyan kudin tafiyar 'ya'yansa.

Firai ministan ya ce ba zai sake maimaita irin haka ba nan gaba.