'Babu kudin da za a yi aiki a Kebbi'

Hakkin mallakar hoto kebbi government
Image caption Atiku Bagudu ya ce gwamnatin Dakingari ta bar 'yan kudaden da ba su taka kara sun karya ba a assusun gwamnati amma kuma ta bar masa bashin sama ga N83m.

Gwamnan jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya ya yi gargadin cewa ayyukan gudanar da gwamnatinsa na dab da tsayawa sakamakon rashin kudi.

Sanata Atiku Bagudu ya ce hakan na faruwa ne saboda gwamnatin da ya gada a watan jiya ta bar 'yan kudaden da ba su taka kara sun karya ba a assusun gwamnati amma kuma ta bar masa bashin sama ga N83b.

Kakakin gwamnan, Alhaji Sani Dododo, ya shaida wa BBC cewa a yanzu suna sayo man da ake sanya wa a motocin gwamnati ne kan bashi saboda rashin kudin balle su yi tunanin biyan albashi.

Sababbin gwamnonin jihohi da dama a Najeriya dai suna zargin magabatansu da sace kudaden jihohin, zargin da magabatan nasu suka musanta.