'Yan gudun hijirar Somalia na cikin tasku

Image caption 'Yan gudun hijira

Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya (WFP) ta ce sai ta rage yawan abinci da kusan rabi na 'yan gudun hijira da ke arewacin Kenya saboda karancin kudi.

Hukumar ta ce za ta rage yawan abincin zuwa kashi daya bisa uku a sansanoni biyu da ke dadaab da kuma Kakuma wadanda nan ne gidanjen 'yan kasar Somalia da 'yan kudancin Sudan.

Lamarin zai shafi kusan mutane rabin miliyan.

Hukumar ta nemi karin taimakon na dala miliyan 12 domin ci gaba da tallafawa 'yan gudun hijirar.

A Nuwambar da ta gabata ne aka tilastawa hukumar rage yawan abinci da kaso daya bisa biyu kafin a samu wani karin tallafin.