Farc ta katse wutar lantarki a Colombia

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Hare-haren na zuwa ne bayan anyi tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Colombia da kungiyar 'yan tawayen Farc.

Dakarun soji sun fitar da wata sanarwar cewa kungiyar 'yan tawayen Farc, a Colombia sun kashe wasu 'yan sanda uku har lahira.

Harin ya janyo katse hanyar samun hasken wutar lantarkin mutane kusan rabin miliyan.

Wadannan hare-haren sun auku duk da tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin kasar da 'yan tawayen.

An yi wannan yarjejeniyar wacce burin ta zaman lafiya ne da samun sauki daga tashe-tashen hankulan da aka shekara 50 ana yi, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 220,000.

Shugaban kasar, Juan Manuel Santos ya mai da martani, inda shi ma ya kai hare-haren bama- bamai a sansanonin su.

Shugaban ya ce hare-haren ba su da ma'ana, inda tun farko mayakan ne suka kai wa wasu 'yan sanda hari a kan titi, sannan kuma daga bisani suka datse wayar da ke samar da wutar lantarki, sakamakon hakan yankin Caqueta suka shiga zama cikin duhu.

A kwana-kwanan nan ma 'yan tawayen Farc sun kai hari wasu gine-ginen gwamnati a kasar, wadanda suka hada da tituna da butatun man fetur.

Masana na kyautata zaton kungiyar 'yan tawayen na kai hare-haren ne domin ta baiwa 'yan kasar haushi, kuma su tirsasawa Shugaba Santos shiga wata yarjejeniyar hadin kai.