An yi nasarar dashen mazakuta na farko

Likita yana tiyata Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Likita yana tiyata

Mutum na farko da aka yi ma dashen mazakuta zai zamo uba, an yi nasarar dashen mazakuta na farko a duniya.

Dan kasar Afrika ta Kudun nan wanda shine mutum na farko da aka yi ma dashen Mazakuta zai zama uba nan ba da jimawa ba.

Likitan da ya yi wannan dashen ne ya sheida ma BBC.

Budurwar mutumen da aka yi ma dashen, ta ba da rahoton cewa ta samu juna-biyu na tsawon watanni hudu, wannan kuwa shine ya nuna cewar dashen ya yi nasara, a cewar Andre Van der Merwe.

Mutumen da aka yi ma dashen dan shekaru 21, wanda aka boye sunan sa, ya rasa mazakutar sa ne a lokacinda aka yi masa kaciya - aka samu kuskure.

Likitocin fida a jami'ar Stellenbosch da asibitin Tygerberg sun kwashe sa'oi 9 suna tiyatar dashen mazakutar.

Dr Van der Merwe ya ce, ya yi matukar gamsuwa lokacinda ya samu labarin cewa budurwar mutumen ta samu juna-biyu kuma ba ta nemi a yi gwaji don gano ubansa ba, saboda babu dalilin ma da zai sanya a yi wata tababa.

"wannan shine abinda muka ayyana, mutumen ya mike tsaye ya yi fitsari tare da yin jima'i. Don haka wannan cigaba ne mai girman gaske a wurin sa." Dr Van der Merwe ya gaya ma BBC.

Ba a yi tunanin mutumen zai gaza samun haihuwa ba, saboda lamarin ya shafi mazakutar sa ne, ba shi da wata matsala da 'ya'yan marainan sa. Likitan ya kara da cewa.

Dr Van der merwe ya yace, tawagar likitocin da suka yi wannan fida ta dashen mazakutar, ba su ma ko hadu, suka sake nazarin nasarar dashen ba, don haka za su yi karin wani dashen.

An bar yaron ne kawai da mazakutar da ba ta wuce tsawon centimeter 1 ba lokacinda aka yi ma sa kaciyar da aka samu kuskure.

Shekarunsa 18 kuma yana jin karfi na yin jima'i a lokacin.

Karin bayani