Kasashen Afrika su daina karban agaji

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Uhuru Kenyatta

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya yi kira ga yan Afirka da su dakatar da karbar agaji daga kasashen waje.

Yayinda yake magana gabanin taron koli na kungiyar tarayyar Afirka a Afirka ta Kudu, ya ce sharuddan da ake gindayawa wajen karbar agajin kan tauye samun cigaba.

Ya ce lokaci yayi da za a hakura da karbar irin wannan tallafi.

Wata wakiliyar BBC a Kenya ta ce kalaman na shugaban kasar fitowa ne ya nuna wani buri, ba wai manufa ce da gwamnatin kasar ta fitar ba.