An haramta wa 'yan sanda saka kakin soji

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Babban hafsan dakarun tsaron Nigeria, Alex Badeh

Rundunar tsaron Nigeria ta haramta wa jami'an tsaro wadanda ba sojoji ba amfani da kakin soja da ake kira 'camouflage'.

Kakakin rundunar, Manjo Janar Chris Olukolade a cikin wata sanarwa ya ce, a yanzu sojin kasa da na sama da na ruwa ne kadai za su saka 'camouflage' ko rigar "bad-da-kama".

Sanarwar ta ce 'yan sanda za su iya saka 'camouflage' idan har ana aikin hadin-gwiwa da sojoji ko kuma wani aiki na musamman domin kwantar da tarzoma.

Olukolade ya ce an bai wa jami'an tsaron da ba sojoji ba ne har zuwa watan Janairun 2016 su janye kakin soji daga hannun jami'ansu.

Wannan matakin ya biyo bayan umurnin da babbar majalisar tsaron kasa ta bayar ne domin hana masu aikata laifuka da suke fakewa da kayan soji su aikata ayyukan asha.