Za a binciki tsofaffin gwamnoni a Nigeria

Hakkin mallakar hoto efcc website
Image caption Sabbin gwamnoni za su binciki tsofaffi a Najeriya

Wasu jihohin Nijeriya sun ce za su binciki tsofaffin gwamnatocin jihohin bisa zargin almundahana da kudaden talakawa.

Sabbin gwamnonin jihohin dai na zargin magabatansu da suka mika masu mulki a watan jiya ne da yin wa-ka-ci-ka-tashi da dukiyoyin jihohinsu, zargin da tsoffin shugabannin ke musantawa.

Gwamnonin sun ce za su kwato kadarori da kudade na gwamnati daga tsofaffin gwamnoni da sauran jami'ai da suke zargi da yin awon-gaba da su.

Jihohin da ke kan gaba a batun binciken sun hada da jihar Bauchi da Plateau da ma jihar Niger.

Sai dai kuma wasu na cewa mafi yawancin shugabannin sabbin gwamnatocin sun rike mukamai a zamanin gwamnatocin da suke zargi.